Gwamnatin Siriya Tana Neman Tattaunawa Da Gwamnatin Mamayar Haramtacciyar Kasar Isra’ila

Fira ministan kasar Siriya ya bayyana cewa: Kasar Siriya zata gudanar da tattaunawa ba na kai tsaye ba da haramtacciyar kasar Isra’ila! Shugaban gwamnatin rikon

Fira ministan kasar Siriya ya bayyana cewa: Kasar Siriya zata gudanar da tattaunawa ba na kai tsaye ba da haramtacciyar kasar Isra’ila!

Shugaban gwamnatin rikon kwarya na kasar Siriya Abu Mohammed al-Julani ya sanar a jiya Laraba cewa: Kasar Siriya zata gudanar da zaman tattaunawa ba na kai tsaye ba da gwamnatin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila ta hanyar masu shiga tsakani domin kwantar da hankulan al’amura da kuma hana bullar rashin kwanciyar hankali a yankin.

Al-Julani ya yi nuni da cewa: “Shisshigin da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ke yi ba bisa ka’ida ba ne, kuma sun bayyana cewa: Siriya ta amince da yarjejeniyar kawo karshen rikici ta shekara ta 1974,” yana mai cewa “Tsarin mulkin kasar Siriya zai tantance ‘yancin mayakan kasashen waje da iyalansu na samun takardar zama ‘yan kasa.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments