An gargadin cewa kasar Libiya za ta shiga wani mummunan yaki saboda rikicin banki!
Kasar Libya dai tana fama da rikicin siyasa da tattalin arziki mai sarkakiya, biyo bayan sauya shekar da gwamnan babban bankin kasar Al-Siddiq Al-Kabir ya yi, wanda ya kai ga kawo cikas ga ayyukan hako mai a yankin gabashin kasar Libya da ke da man fetur mafi girma a nihiyar Afirka.
A makon da ya gabata ne dai Majalisar Gudanar da Shugabancin kasar ta sanar da korar Al-Siddiq Al-Kabir tare da maye gurbinsa da Muhammad Al-Shukri a matsayin magajinsa.
Matakin dai ya haifar da ce-ce-ku-ce a cikin fargabar sake barkewar wani sabon yaki a kasar, musamman ganin yadda dukkanin bangarorin siyasar kasar suka yi riko da matsayinsu tare da yunkurin sojojin kasar a kwanakin baya na tsoma baki a wasu harkokin kasar.