Gwamnatin Lebanon Ta Yi Allawadai Da Hare-Haren Isra’ila A Beirut

Ministan harkokin wajen kasar Lebanon a gwamnatin rikon kwarya ta kasar Abdullah Bou Habib, ya yi Allah wadai da harin da Isra’ila ta kaddamar kan

Ministan harkokin wajen kasar Lebanon a gwamnatin rikon kwarya ta kasar Abdullah Bou Habib, ya yi Allah wadai da harin da Isra’ila ta kaddamar kan kasar, yana mai bayyana hakan a matsayin “laifi na yaki.”

Ministan harkokin wajen kasar Labanon, Abdallah Bou Habib, ya bayyana a jiya Juma’a cewa “Isra’ila” ba za ta iya mayar da mutanenta da suka rasa matsugunansu ta hanyar amfani da makamai zuwa matsugunan arewaci ba, sai dai za ta kara wasu  da dama su rasa matsugunansu.

Bou Habib ya bayyana a cikin jawabinsa a gaban kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya cewa, bayan harin da Isra’ila ta kai kan kayayyakin sadarwa a kasar Lebanon, “babu wani mutum a wannan duniya da ya tsira,” ya kara da cewa “Hare-haren Isra’ila sun zarce tunanin duk wani mutum mai hankali, ta yadda lamarin ya zama tamkar wani hauka da rashin sanin abin da ya kamata.

Kwamitin Sulhu yana da girma a gaban dukkan mutanen duniya, ko dai kwamitin sulhun ya bukaci Isra’ila ta dakatar da ta’addanci da yaki a kowane bangare, ko kuma mu zama masu shaidar karya a kan wasu ayyukan nata a nan gaba.

Ya kuma jaddada cewa, “Isra’ila” ba ta bin dokokin kasa da kasa da na jin kai, kuma tana yin watsi da hakkin bil’adama, saboda ba a tuhumar ta da laifukan da ta aikata.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments