Shugabna Pual Kagame na kasar Rwanda ya bayyana cewa ba zai dakatar da goyon bayana da yake bawa kungiyar yan tawaye ta M23 ba, wadanda a cikin yan kwanakin da suka gabata sun kwace wurare da dama a arewacin Kivu na kasar DMC daga cikin har da birnin Goma babban birnin lardin.
Shafin yanar gizo na ‘Afirca News’ ya nakalto kagami yana cewa ya a shirye yake ya shiga yaki da kowa saboda kare matsayinsa.
A yau Alhamis dai mayakan M23 sun kammala kwace iko da birnin Goma babban birnin yankina kuma a halin yanzu sun nosa zuwa garin Bukavu babban birnin lardin Kivu ta kudu. Wannan dai shi yaki mafi girma wadanda ake yi a yankin KIvi tun shekara ta 2012.
Kasashen turai wadanda suke da manya-manyan kamfanonin hakar ma’adinai a yankin sun yi barazana ga shugaba kagami kan cewa zau dakatar da tallafin da suke basu. . Kasar Jamani ta ce zata dakatar da dalar Amurka miliyon 40 da take son bawa kasar ta Ruwanda idan ta ci gaba da goyon bayan kungiyar ta M23.