Gwamnatin Kasar Guinea Ta Yi Wa Musa Dadis  Camara Afuwa

Shugaban gwamnatin soja na kasar Guinea Conakry Janar Mamadi Doumbouya ne ya yi wa tsohon shugaban sojan kasar Camara afuwa bayan da aka yanke masa

Shugaban gwamnatin soja na kasar Guinea Conakry Janar Mamadi Doumbouya  ne ya yi wa tsohon shugaban sojan kasar Camara afuwa bayan da aka yanke masa zaman gidan kurkuku bisa laifin kisan kiyashin da ya faru a 2009 a birnin Conakry.

Kafafen watsa labarun kasar ta Guinea ne su ka sanar da afuwar da shugaba Mamadi ya yi wa Camara bisa dalilai na rashin lafiya.

Bugu da kari kakakin fadar shugaban kasa Janar Amara Camara wanda ya yi sanarwar ya ce, an yi hakan ne bisa shawarar da ma’aikatar shari’a ta gabatar.

Camara dai ya mulki kasar ta Guinea ne daga 2008-2009, an kuma yi masa shari’a ne a watan Yuli na 2024, saboda yadda a zamanin mulkin nashi aka yi amfani da karfi wajen murkushe ‘yan hamayya da su ka yi wani taro a cikin filin wasan kwallon kafa na Conakry.

Fiye da mutane 150 ne dai su ka kwanta dama, kuma jami’an tsaron kasar su ka yi wa mata fiye da 100 fyade.

Shari’ar da aka yi wa Camara wacce ta sami cikakken goyon bayan MDD, ta same shi da lafin gajiyawa wajen hukunta masu laifi.

Matakin na gwamantin yanzu ya biyo bayan shirinta na biyan diyya ga iyalan wadanda aka kashe da kuma yi wa illa.

Sai dai kungiyoyin kare hakkin bil’adama a kasar suna sa alamun tambaya akan wannan matakin na yi wa adalci Karen tsaye.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments