Ministan Harkokin Cikin Gida Ya Yi Watsi Da Shelanta Samun Nasara Da Dantakara Isa Bakari Ya Yi
Ministan harkokin cikin gidan kasar Kamaru Paul Atanga Nji ya yi watsi da yadda dan takarar shugabancin kasar Isa Tchiroma Bakari ya shelanta kansa a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa, ya kuma yi kira ga shugaban kasar Paul Biya da ya amince da shan kaye.
Ministan harkokin cikin gidan na kasar Kamaru ya zargi Issa Bakari da cewa yana da wani shiri na kokarin kona kasar Kamaru ta hanyar taimakon kasashen waje.
A makon da ya shude ma dai Atanga Nji ya yi gargadi kar wanda ya fitar da sakamakon zaben, domin yin hakan zai zama daidai da cin amanar kasa.
A karkashin dokokin zabe na kasar Kamaru kotun tsarin Mulki ce kadai take da hakkin sanar da sakamakon zabe.
A ranar 12 ga watan nan na Oktoba ne dai Issa Tchiroma ya bayyana kansa a matsayin wanda ya lashe zaben da aka yi na shugaban kasa.
Shi dai Tchiroma wanda yake cikin shekaru na 70, ya taba rike mukamin mai Magana da yawun gwamnati, haka nan kuma ministan samar da ayyuka a karkashin gwamnatin Paul Biya.
Paul Biya wanda ya haura shekaru 90, ya kwashe shekaru 40 akan karagar Mulki da hakan ya mayar da shi shugaba na biyu a kasar ta Kamaru tun bayan samun ‘yanci daga Faransa. Ya hau karagar Mulki ne dai a 1982, bayan da ya kwace Mulki a hannun Ahmad Ahidjo da ya tafi waje neman magani.