Gwamnatin Amurka Tana Shirin Dakatar Da Bada Kudaden Tallafi Don Samar Da Wasu Magunguna

Gwamnatin kasar Amurka tana shirin dakatar da bada kudade ga hukumar GAVI wacce take samar da alluran riga kafi don tallafawa kasashe masu tasowa daga

Gwamnatin kasar Amurka tana shirin dakatar da bada kudade ga hukumar GAVI wacce take samar da alluran riga kafi don tallafawa kasashe masu tasowa daga ciki har da tarayyar Najeriya.

Jaridar Daily Trus ta Najeriya ta nakalto wata sanarwa daga hukumar USAID bayar inda take cewa gwamnatin shugaba Donal  Trump yana son janye tallafin da kasarsa ke bayarwa don wannan shirin, wanda yake yakar cutar Malaria da wasu cututtuka a wadannan kasashe.

Labarin ya kara da cewa za’a dakatar da ayyukan samar da magunguna da alluran riga kafa har guda 5,341 idan an dakatar da tallafi, wanda yake cinye dalar Amurka biliyon 75 a ko wace shekara. A halin yanzu dai hukumar ta USAID ta bada dalar Amurla biliyon 48, don samar da wasu magungunan da alluran riga kafi n awannan shekarar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments