Gwamnatin Amurka Ta na Son Katse Dangantakan Da Ke Tsakanin Rasha Da Iran

Jakadan Amurka na musamman kan kasashen Rashad Ukraine ya bayyana cewa Amurka tana kokarin ganin ta kawo karshen dukkan dangantakar da ke tsakanin kasashen China

Jakadan Amurka na musamman kan kasashen Rashad Ukraine ya bayyana cewa Amurka tana kokarin ganin ta kawo karshen dukkan dangantakar da ke tsakanin kasashen China da Rasha da kuma JMI.

Tashar talabijian ta Presstv a nan Tehran ta nakalto, Keith Kellogg ya na fadar haka a taron Munich na tsaro a jiya Asabar.

Ya kuma kara da cewa gwamnatin Trump tana aiki dare da rana don ganin ta wargaza dukkan dangantaka da ke tsakani Iran da Rasha da kuma China.

Jakadan ya kara da cewa dangantaka da ke tsakanin wadannan kasashen da JMI babu ita a shekaru 4 da suka gabata. Amma shugaba Donal Tromp yana aiki a kan haka. don ganin an katse dangantakar wadannan manya-manyan kasashe da JMI. Saboda barin Iran ita kadai.

Manufar dai ita ce tabbatar da cewa duk kasashen duniya sun maida Iran saniyar ware.

A sannan ne kuma takunkuman tattalin arziki  mafi tsananin da gwamnatin Trump ta dorawa JMI zasu yi aiki. A sannan ne gwamnatin kasar Iran zata durkusar.

Kasar Iran dai tana da dangantaka ta musamman kuma masu dogon zango da wadannan kasashe biyu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments