Guterres Ya Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Taimaka Wa Sudan

Babban sakataren MDD Antonio Guterres  wanda ya halarci taron kungiyar tarayyar Afirka AU da aka bude a birnin Addis Ababa na kasar Habasha, ya kira

Babban sakataren MDD Antonio Guterres  wanda ya halarci taron kungiyar tarayyar Afirka AU da aka bude a birnin Addis Ababa na kasar Habasha, ya kira yi kungiyoyin kasa da kasa da su kai daukin gaggawa ga kasar Sudan ta fuskar bada kayakin agaji.

Guterres ya nanata muhimmancin kai kayakin abinci da sauran kayakin da ake bukatuwa da su, domin taimakawa mutanen kasar ta Sudan da yaki ya daidaita.

Babban magatakardar MDD ya yi ishara da rawa ta jarunta da kungiyoyin mata  suke yi a cikin yanayi mai hatsari,tare dayin kira da a kare rayukan fararen hula.

Har’ila yau ya yi kira da a kawo karshen shigar da makamai zuwa kasar ta Sudan da bai wa zaman lafiya dama, a cikin watan Azumin Ramadana mai shigowa.

A mako mai zuwa ne dai MDD za ta kaddamar da gidauniyar agaji ta neman kudaden da za su kai dala biliyan 6 domin taimakawa miliyoyin mutanen Sudan da suke zaman hijira a kasashe makwabta.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments