Guteress : ba wadan zai ci ribar yakin cinikayya

Sakatare janar na majalisar dinkin duniya ya ce ba wanda zai ci ribar yakin cinikayya a yayin da ake ta cacar baka kan harajin fito

Sakatare janar na majalisar dinkin duniya ya ce ba wanda zai ci ribar yakin cinikayya a yayin da ake ta cacar baka kan harajin fito da shugaban Amurka Donald Trump ya lafta wa duniya.

 Antonio Guitess ya yi wannan gargadin ta bakin kakakinsa inda ya yake bayyana cewa, “ba wanda ke yin nasara a yakin na cinikayya.

” Yana mai cewa, a yayin da ake samun karuwar adawa daga sassa daban daban, shugaban Amurka Donal Trump a ranar Laraba ya rattaba hannu kan wani umarnin zartarwa kan abin da yake kira “harajin fito na ramuwar gayya,” wanda ya sanya kashi 10 cikin dari na mafi karancin harajin fito, da karin sama da haka kan wasu abokan cinikayyar kasar.

A wani batun kuma, taron MDD kan cinikayya da ci gaba wato UNCTAD, ya yi gargadi a cikin wata sanarwa a ranar Juma’a cewa, harajin fito da Amurka ta sanya zai cutar da kasashe masu rauni, kana “tsarin cinikayya na duniya ya shiga wani mataki, wanda ke yin barazana ga ci gaba, da zuba hannun jari, musamman ga kasashe masu rauni,” yayin da manyan kasashe masu karfin tattalin arziki ke shirin sanya sabbin harajin fito a nasu bangare a matsayin ramuwar gayya ga matakin na shugaban Amurka.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments