Guinea: An Tsayar Da Ranar  28 Ga Disamba Domin Zaben Shugaban Kasa

Kwanaki kadan bayan da aka gudanar da zaben raba gardama akan sabon tsarin mulkin kasar, mahukuntan sojan kasar sun ayyana ranar yin zaben shugaban kasa

Kwanaki kadan bayan da aka gudanar da zaben raba gardama akan sabon tsarin mulkin kasar, mahukuntan sojan kasar sun ayyana ranar yin zaben shugaban kasa da zai zama na farko a cikin shekaru 4 na mulkin soja.

Sanarwar tsayar da ranar yin zaben shugaban kasar dai, an yi ta ne ta hanyar dokar soja a ranar Asabar din da ta gabata.

Sakamakon kuri’ar raba gardamar da aka yi a ranar 21 ga watan nan na Satumba, ta nuna cewa kaso 89% na wadanda su ka kada kuri’ar, sun nuna amincewa da sabon tsarin mulkin.

Har ila yau, wata kididdiga ta nuna cewa kaso 86% na wadanda su ka cancanci yin zabe ne su ka kada kuri’a.

Jam’iyyun hamayyar kasar ta Guinea sun kira yi mutane da su kauracewa kada kuri’unsu akan sabon tsarin mulkin da su ka kira shi da ‘dodorido,kuma an tsara yadda sakamakon zai kasance.

A karkashin sabon tsarin mulkin, shugaban mulkin soja Janar Mamady Doumbouya zai tsaya takarar shugabancin kasar. A baya,lokacin juyin mulkin da ya jagoranta, Janar Doumbaya ya yi alkawalin cewa ba zai tsaya takarar shugabancin kasar ba.

Har ila yau an kara tsawon wa’adin shugabancin kasar daga shekaru 5 zuwa 7, za kuma a iya sabunta shi sau daya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted