Shugaban hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya, Rafael Grossi ya ce ya yi tattaunawa mai ma’ana da jami’an Iran a yayin ziyarar da yak ai kwanan nan a Tehran kuma yana fatan za a ci gaba da gudanar da irin wannan hulda a nan gaba.
Mista Grossi, ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai a Vienna bayan ya ziyarci Iran.
Grossi ya ce tarurrukan nasa sun yi armashi” wanda zai kara inganta huldar dake tsakanin hukumar da Iran.
Ya ce ya tattauna akan wasu mahimman batutuwa tare da shugaban kasar Iran da kuma ministan harkokin wajen kasar.
Shugaban hukumar ta IAEA ya ce Iran ta amince ta kayyade yawan sinadarin uranium da ta tace da kashi 60 cikin 100 tare da karbar sabbin jami’an da hukumar ke bukata a Iran.
Grossi dai ya je Tehran ne domin tattaunawa da mahukuntan da nufin warware batutuwan da ake takaddama akansu tsakanin hukumar.
Tuni dai manyan kasashen yammacin duniya suka gabatar da wani kuduri kan abin da suka bayyana a matsayin rashin hadin kai na Iran ga hukumar IAEA a taron kwamitin gwamnonin hukumar.
Saidai ministan harkokin wajen Iran ya yi gargadin mayar da martani idan kwamitin ya zartar da kudurin.