Gidauniyar Hind Rajab ta kai karar Isra’ila kan harin jirgin ruwan Madleen

Gidauniyar Hind Rajab (HRF), mai rajin kare hakkin Falasdinawa, ta shigar da kara kan laifukan yaki bayan farmakin da sojojin ruwan Isra’ila suka kai kan

Gidauniyar Hind Rajab (HRF), mai rajin kare hakkin Falasdinawa, ta shigar da kara kan laifukan yaki bayan farmakin da sojojin ruwan Isra’ila suka kai kan jirgin ruwan agaji na Birtaniya Madleen a ruwan kasa da kasa a yammacin Lahadi.

Koken dai ya shafi rundunar sojin ruwa ta Isra’ila Shaytet 13 da kwamandan ta, Vice Admiral David Saar Salama.

Gidauniyar ta HRF ta yi kira da a gaggauta sakin masu fafutuka 12 da ake tsare da su, ciki har da mai fafutukar kare muhalli Greta Thunberg, dan wasan kwaikwayo Liam Cunningham, da Rima Hassan ta faransa, wadanda ke hannun Isra’ila.

Jirgin ruwan na Madleen, na kungiyar Freedom Flotilla Coalition, na dauke da kayayyakin jinya, da abinci, da madarar jarirai, da sauran kayan agaji da aka nufi zuwa Gaza a lokacin da aka kama shi fiye da mil 60 a tekun ruwa.

Madleen, wanda ya tashi daga Sicily, an dora masa alhakin isar da kayayyakin jin kai zuwa Gaza wanda Isra’ila ta yi kawanya.

Sojojin Isra’ila sun shiga cikin jirgin, sun kame fasinjoji tare da kwace kayan agajin.

Dama Irin wannan lamari ya faru a watan Mayun 2025, lokacin da jiragen Isra’ila marasa matuka suka kai hari kan wani jirgin ruwa dauke da Greta Thunberg a gabar tekun Malta.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments