Jamhuriyar Musulinci ta Iran, ta bayyana cewa tace uranium din ta tamakar jan layi ne a tattaunawar dake wakana tsakaninta da Amurka.
Mataimakin ministan harkokin wajen kasar ne Kazem Gharibabadi ya bayyana hakan, inda ya ce hakkin Jamhuriyar Musulunci ta Iran ne inganta sinadarin Uranium, yana mai jaddada cewa, wannan batu a matsayin jan layi a tattaunawar da Amurka.
Mista Gharibabadi ya bayyana haka ne a yayin taron kwamitin majalisar dokoki kan tsaron kasar da manufofin ketare, inda ya yi wa ‘yan majalisar bayani kan shawarwari zagaye na biyu tsakanin Tehran da Washington, wanda ya gudana a Rome, babban birnin kasar Italiya.
Jami’in na iran ya kara da cewa tawagar kasar ta jaddada matsayinta na cewa Iran ba ta neman kera makaman kare dangi, inda ya bayyana cewa ayyukan nukiliyar Iran na zaman lafiya ne gaba daya.
Mataimakin ministan harkokin wajen na Iran ya kuma jaddada cewa, daya daga cikin manyan makasudin shawarwarin shi ne cimma nasarar dage takunkumin da aka sanya wa iran gaba daya da suka hada da na majalisar dokokin Amurka da kuma umarnin zartarwar takunkuman matsin lamba da shugaba Donald Trump ya sanya wa hannu.
Kawo yanzu AMurka da Iran sun gudanar da shawarwari har guda biyu ka batun shirin nukiliyar kasar ta Iran, kuma dukkan bagarorin sun bayyana tattaunawar da mai kyakyawan fata.
A ranar Asabar mai zuwa bagarorin zasu sake ganawa a karo na uku, bayan wacce sukayi a Oman da kuma Italiya.