GCC Tayi Allah wadai Da Kisan Kiyashin Da Isra’ila Ke Yi A Gaza

Shugabannin kasashen yankin Gulf sun jaddada kiransu na tsagaita bude wuta cikin gaggawa a zirin Gaza bayan ganawar da suka yi a Kuwait ranar Lahadi.

Shugabannin kasashen yankin Gulf sun jaddada kiransu na tsagaita bude wuta cikin gaggawa a zirin Gaza bayan ganawar da suka yi a Kuwait ranar Lahadi.

Kasashen sun kuma yi maraba da sammacin kame Netanyahu na Isra’ila da tsohon ministan tsaro Yoav Gallant da kotun ICC ta yi, suna masu watsi da ikirarin Isra’ila na cewa tana kare kan ta ne.

Shugabannin sun kuma yi Allah wadai da muggan laifukan da sojojin mamaya na Isra’ila suka aikata a zirin Gaza a matsayin wani bangare na kisan kare dangi da ya hada da kisan fararen hula, azabtarwa, tilasta gudun hijira da kwasar ganima.

Ko a baya bayan nan kusan Falasdinawa 100 suka rasu a wani mummunan “kisan kiyashi” da Isra’ila ta aikata a cikin kwana guda a Gaza, kamar yadda Hukumar Kare Farar Hula ta Gaza ta sanar.

kimanin falasdinawa 44,400 ne sukayi shahada a hare-haren Isra’ila kan zirin Gaza tun bayan harin ba-zata na kungiyar Hamas kan Isra’ila a ranar 7 ga watan Oktoban 2023.  Yaƙin da Isra’ila take yi a Gaza — wanda ya shiga kwana na 422 a yau — ya kashe Falasɗinawa fiye da 44,382 da jikkata fiye da mutum 105,142. A Lebanon kuwa, Isra’ila ta cim ma yarjejeniyar tsagaita wuta bayan kashe mutum 3,961 tun daga Oktoban bara.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments