Gaza: Falasdinawa 7 Sun Yi Shahada Da Safiyar Yau Asabar

Da safiyar yau Asabar Falasdinawa 7 sun yi shahada sanadiyyar harin da HKI ta kai a yankin Gaza. Sojojin HKI sun kai harin ne a

Da safiyar yau Asabar Falasdinawa 7 sun yi shahada sanadiyyar harin da HKI ta kai a yankin Gaza.

Sojojin HKI sun kai harin ne a kan sansanin ‘yan hijira na unguwar ” al-Sabrah” a cikin birnin Gaza, da hakan ya yi sanadiyyar shahadar Falasdinawa 5 a iyalai daya na Dulaibh. Shahidan su nel Saqar Ahmad Fu’ad dulaibh, da matarsa Hindu, da ‘ya’yansu Ahmad, Hamzah, da Abdulazizi.

Haka nan kuma ‘yan sahayoniyar sun kai wasu hare-haren ta jirgin sama maras matuki a unguwar “Tuffah” dake birnin Gaza, da ya yi sanadiyyar shahadar mutum daya.

Su ma jiragen ruwan HKI sun kai wasu hare-haren munanan a garin Rafah da ya yi sanadiyyar shahadar Muhammad Sa’id al-Burudawil.

A tsakiyar birnin Gaza, ma dai ‘yan sahayoniyar sun kai wasu hare-hare da manyan bindigogi da ya yi sanadiyyar shahadar karamin yaron Bafalasdine guda.

A wani gefen hukumar Gaza ta sanar da cewa yunwa, tana barazana ga rayuwar kananan yaran da sun kai 65,000 saboda ci gaba da hana shigar da kayan abinci cikin yankin na Gaza, da HKI take yi, na tsawonn watanni 2 a jere.

Tsawon kwanaki 40 kenan da dukkanin gidajen burodi a cikin yankin na Gaza su ka rufe kofofinsu saboda rashin fulawa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments