Gaza: Yawan Mutanen Da Suka Yi Shahada Sanadiyar Hare-Haren HKI Ya Dara 400

HKI ta keta yarjeniyar tsagaita wuta a Gaza, a jiya inda ta kai hare-hare masu yawa, wadanda suka yi sanadiyar mutuwar mutane fiye da 300

HKI ta keta yarjeniyar tsagaita wuta a Gaza, a jiya inda ta kai hare-hare masu yawa, wadanda suka yi sanadiyar mutuwar mutane fiye da 300 ya zuwa safiyar yau.

Tashar talanijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa, jiragen yakin HKI sun kai hare-haren a kan yankunan zirin Gaza da dama, kuma yawan mutanen da suka yi shahada ya zuwa yanzu ya kai 342 kumamafi yawansu mata da yara ne.

Labarin ya kara da cewa a garin Khan Yunus na kudancin Gaza jiragen yakin HKI sun kashe falasdinawa 77 sannan falasdinawa akalla 20 suka kashe a birnin Gaza. SAMA kamfanin dillancin labaran Falasdinawa ya bayyana cewa daruruwan Falasdinawa sun rasa rayukansu, kuma har yanzun ana neman wasu a wuraren da yahudawan suak kai hare hare.

Tashar talabijin ta Aljazeera ta bada labarin cewa hare-haren yahudawan sun game dukkan zirin gaza kuma sai da suka girgiza yanking aba daya.

Wasu masana suna ganin sojojin yahudawan sun yi amfani da sabbin makamai masu tun 20 wadanda gwamnatin Trump ta bawa HKI bayan ya dare kan kujerar shugabancin kasar ta Amurka.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments