Gaza : Spain ta bukaci kasashen duniya su kakabawa Isra’ila takunkumi

Kasar Spain ta bukaci kasashen duniya dasu kakabawa Isra’ila taklunkumi saboda ci gaba da yin fatali da kiraye-kirayen da ake matana tadakatar da yakin da

Kasar Spain ta bukaci kasashen duniya dasu kakabawa Isra’ila taklunkumi saboda ci gaba da yin fatali da kiraye-kirayen da ake matana tadakatar da yakin da take a Gaza.

Ministan harkokin wajen Spain José Manuel Albares ya ce kamata ya yi kasashen duniya su kakabawa Isra’ila takunkumi domin kawo karshen munanan hare-haren soji a zirin Gaza da aka yi wa kawanya.

Shugaban diflomasiyyar Spain yana magana ne gabanin wani babban taron kasashen Turai da na Larabawa da za a yi ranar Lahadi a Madrid.

“Dole ne mu komai, don kawo karshen wannan yakin,” in ji shi.

M.Albares ya bukaci a shigar da agajin jin kai, ba tare da wani sharadi ba, ba tare da tsangwama ba, ta yadda Isra’ila ba ta yanke shawarar wanda zai iya ci da wanda ba zai iya ba.

Taron na ranar Lahadi, wanda ya hada da wakilan kungiyar hadin kan kasashen Larabawa da kungiyar hadin kan kasashen musulmi, na da nufin ingiza bukatar da wasu kasashen duniya ke mikawa  na samar da kasashe biyu da bufin kawo karshen rikicin da aka kwashe shekaru anayi.

Isra’ila dai na fuskantar matsin lamba daga kasashen duniya, musamman daga kawayenta na kut-da-kut kan ta dakatar da kai hare-haren da take kaiwa da kuma ba da damar kai agajin jin kai a Gaza.

A wannan makon ne Tarayyar Turai ta kada kuri’ar amincewa da sake duba yarjejeniyar kungiyar da Isra’ila.

A halin da ake ciki kuma, a baya-bayan nan kasar Sweden ta ce za ta matsa wa kungiyar mai kasashe 27 lamba kan ta kakaba takunkumi kan ministocin Isra’ila, yayin da Birtaniyya ta dakatar da tattaunawar cinikayya cikin ‘yanci da Isra’ila.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments