Jiragen yakin HKI sun harba makamai masu linzami guda biyu akan ginin asibitin Ma’amadani dake Gaza. Harin ya yi sanadiyyar rushewar wasu bangarori da su ka hada dakunan yin gwaje-gwaje da kantin sayar da magani.
Saboda hare-haren na Isra’ila a wannan asibitin, da akwai gwamman marasa lafiya da suke kwance a kasa a waje, yayin da wasu kuma suke kwance wajen asibiti.
Kungiyar Hamas ta bayyana harin da sojojin HKI su ka kai wa asibitin da cewa wani sabon laifi ne na dabbanci da ‘yan sahayoniyar suka tafka a Gaza.
Haka nan kuma Kungiyar ta Hamas ta zargi Amurka da cewa ita ce take bai wa HKI haske akan tafka laifukan da take yi a Falasdinu.
Bugu da kari kungiyar ta Hamas ta kuma yi mamaki akan yadda kungiyoyin kasa da kasa da su ka hada da MDD suke yin shiru akan laifukan da ake tafkawa da ba su da tamka a wannan zamanin, akan asibitoci da cibiyoyin kiwon lafiya da cutar da marasa lafiya da korarsu daga asibiti zuwa kan tituna.