A wani sabon kisan kiyashin da sojojin HKI suka aikata a yau Asabar a sansanin yan gudun hijira na Al-mawasi da ke kusa da garin Khan Yunus na zigin Gaza, akalla mutane 100 ne, mafi yawansu yara sun yi shahada, sannan a kalla wasu 300 sun ji rauni.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa kafin haka Gwamnatin HKI ta shelanta wannan sansanin yan gudun hijira a matsayin tudun na tsara ga Falasdinawa a Gaza, amma a safiyar yau da misalign karfe 10.30 jiragen yakin HKI samfurin F16 suka cilla malamai masu linzami har guda 9 a kan sansanin.
Banda haka sun biyo da jiragen yaki wadanda ake sarrafasu daga nesa suka cilla makamai kan jami’an agajin da suka zo ceton wadanda suke da sauran numfashi a hari na farko. Su ma an kashe da dama daga cikinsu.
Labarin ya kara da cewa an kai wadanda suka ji rauni zuwa Asbitin Kuwait da ke yankin.
Suhaib Al-Hams shugaban asbitin Kuwait a Gaza ya bayyana cewa asbitin bai da kayakin aikin karbo wannan adadi mai yawa na majinyata. Don haka suna ji suna ganin wasu zasu subar da jinni har su bar duniya ba tare da sun iya yi masu wani abu ba.
A yau asabar ce ake cika kwanaki 281 da fara yaki a gaza, wato watanni 9 da yan kwanaki kenan. Ya zuwa yanzu dai sojojin HKI sun kai falasdinawa 38,345 ga shahada a yayinda wasu dubban kuma suka ji rauni, mafi yawansum mata da yara.