Gaza: Fararen hula 22 sun yi shahada a hare-haren Isra’ila a daren jiya

Hare-haren da Isra’ila ta kai a zirin Gaza a daren jiya ya yi sanadiyar shahadar Falasdinawa da dama tare da jikkata wasu masu tarin yawa,

Hare-haren da Isra’ila ta kai a zirin Gaza a daren jiya ya yi sanadiyar shahadar Falasdinawa da dama tare da jikkata wasu masu tarin yawa, yayin da jiragen yakin Haramtacciyar Kasar Isra’ila ke ci gaba da kaddadamar da munanan hare-hare a kan a yankuna da dama na Zirin da aka yi wa kawanya, da suka hada da gidajen farar hula da tantunan da aka kafa a mafaka  ga iyalan da suka rasa matsugunansu.

A cewar wakilin Al Mayadeen, akalla Falasdinawa biyar ne suka yi shahada, wasu kuma suka jikkata bayan da jiragen saman Isra’ila suka yi ruwan bama-bamai a wani tanti da ke a yankin Tal, kudu maso yammacin Deir al-Balah a tsakiyar Gaza.

A sansanin Nuseirat na yammacin Gaza, wani jirgin sama mai saukar ungulu na Isra’ila ya kai hari kan wani gida da ke hasumiyar al-Salhi kusa da unguwar  Abu Serrar, inda ya kashe Anas Abdul Rahman al-Jammal, da matarsa, da ‘ya’yansu mata biyu. Harin ya kuma yi sanadiyyar jikkata wasu fararen hula.

An samu karin hasarar rayuka bayan harin da Isra’ila ta kai kan iyalan da suka rasa matsugunansu a sansanin ‘yan gudun hijira na al-Bureij, da ke tsakiyar zirin Gaza.

A kudancin zirin Gaza, hare-haren da jiragen yakin Isra’ila suka kai a yankin al-Mawasi dake yammacin Khan Younis, sun yi sanadin shahadar da dama daga cikin fararen hula da suka hada da wani karamin yaro mai suna Amir Mansour mai shekaru 6 tare da mahaifiyarsa.

Hakazalika jiragen yakin haramtacciyar kasar Isra’ila sun yi ruwan bama-bamai a sansanin Khan Younis da ke yammacin Gaza, inda suka kashe Ahmad Rubhi Abu Sahloul, da matarsa, da ‘ya’yansu bayan sun kai hari a gidansu da ke unguwar al-Qatatwa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments