Gaza : EU ba ta gamsu da sabon tsarin raba agaji na Amurka da Isra’ila ba  

Kunngiyar Tarayyar Turai, ta ce ba ta gamsu da sabon tsaron raba kayan agajin jin kai da Amurka da Isra’ila ke shirin aiwatarwa a Gaza.

Kunngiyar Tarayyar Turai, ta ce ba ta gamsu da sabon tsaron raba kayan agajin jin kai da Amurka da Isra’ila ke shirin aiwatarwa a Gaza.

Babbar jami’ar diflomasiyyar kungiyar, Kaja Kallas, ta bayyana cewa Tarayyar Turai ba ta goyon bayan sabon tsarin raba agajin jin kai da Amurka da Isra’ila ke kokarin aiwatarwa wanda ke kaucewa hadin gwiwa da Majalisar Dinkin Duniya da sauran kungiyoyin agaji.

Kallas, ta kuma bayyana cewa hare-haren da Isra’ila ke kai wa a Gaza sun wuce abun da suke bukata wajen yakar Hamas, a yayin da adadin wadanda suka rasa rayukansu ke ci gaba da karuwa.

Tun bayan da Isra’ila ta dawo da yaki a watan Maris bayan ruguza  yarjejeniyar tsagaita wuta da ta cimma da Hamas, kimanin mutum 3,924 ne sukayi shahada a cewar ma’aikatar lafiyar a Gaza.

Isra’ila dai ta ci gaba da cewa tana kai hare-haren ne don kawar da Hamas da ceto wadanda kungiyar ke garkuwa da su.

Sai dai hare-haren kwanan nan sun yi sanadin mutuwar fararen hula da dama.

Jawabin Kallas ya biyo bayan kalamman da Firaministan Jamus, Friedrich Merz, ya yi, inda ya bayyana cewa “a yanzu ba ya fahimtar manufar Isra’ila a Gaza.”

Isra’ila dai ta fara kai farmaki a Gaza ne bayan harin ba zata na Hamas a ranar 7 ga Oktoban 2023, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane akalla 1,200 da kuma sace wasu 251, sai kuma mutane sama da 54,084 a hare-haren ramuwar gayya na Isra’ila.  

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted