A Isra’ila dubban ‘yan kasar ne suka gudanar da zanga-zanga a birnin Tel Aviv, suna masu kira da a kai ga sasanta domin a saki wadanda ake garkuwa da su a Gaza.
Masu zanga-zangar suna masu kira da a kara kaimi wajen ganin an sako fursunonin da ake tsare da su a Gaza.
Masu zanga-zangar sun taru a wajen hedkwatar sojojin kasar da wasu gine-ginen gwamnati a ranar Asabar, inda suke rera taken nuna adawa da Netanyahu tare da yin kira gare shi da ya cimma matsaya da kungiyar Hamas don tabbatar da dawo da kusan fursunoni 100 da ake tsare da su a yankin da yaki ya daidaita.