Gabon: An Daure Mata Da ‘Dan  Tsohon Shugaban Kasa Bongo Shekaru 20 A Gidan Yari

Matar tsohon shugaban kasar Gaba, Sylvia Bongo da kuma dansa Nuruddin Bongo za su yi zaman kaso na tsawon shekaru 20 saboda samunsu da laifin

Matar tsohon shugaban kasar Gaba, Sylvia Bongo da kuma dansa Nuruddin Bongo za su yi zaman kaso na tsawon shekaru 20 saboda samunsu da laifin almubazzaranci da kudin kasa.

Kotun da ta yi shari’ar ta yanke hukunci ne akan iyalan tsohon shugaban kasar Ali Bongo  ba tare da suna gabanta ba. Kotun dai an kafa ne domin yin binciken laifuka da suke da alaka da barnata dukiyar kasa.

Kotun ta sami mai dakin tsohon shugaba Bongo, Sylvia Bongo Ondimba da laifin almundahana da dukiyar kasa da kuma yin takardu na jabu.

Shi kuwa  Nuruddin Bongo an same shi ne da laifukan da su ka hada da runton bai wa kai mukamai,wanke kudaden haram da mayar da su halaliya, sannan da shirya makarkashiya domin aikata laifuka.

Kowane daya daga cikinsu an kuma ci tararsu da kudin da sun kai saifa miliyan 100.

Dan shugaban kasar ta Gabon Nuruddin Bongo ya kore cewa ya yi almundahanar kudin kasar, kuma ya yi alkawalin ci gaba da kare hakkinsa har bayyanar gaskiya.

Mai shigar da kara na gwamnati ya bukaci ganin kotun ta musamman ta yanke wa Sylvia da Nuruddin hukuncin zaman kurkuku na shekaru 20, saboda daukar duniyar al’umma da mayar da ita ta kashin kai.

A 2023 ne dai aka yi juyin Mulki a kasar ta Gabon wanda ya kawo karshen mulkin iyalan Bongo na tsawon shekaru 55.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments