Gabashin DRC : Félix Tshisekedi Ya Sanar Da Maida Da Martani”

Shugaba Felix Tsisekedi na Jamhuriyar Demokuradiyyar Congo ya bukaci hadin kai na al’ummar kasar tare da sanar da mayar da martini kan rikicin gabashin kasar

Shugaba Felix Tsisekedi na Jamhuriyar Demokuradiyyar Congo ya bukaci hadin kai na al’ummar kasar tare da sanar da mayar da martini kan rikicin gabashin kasar dake da nasaba da kungiyar ‘yan tawaye ta M23.

A yayin wani jawabi ga al’ummar kasar, shugaban na Kongo ya yi kira da a hada kai tare da ba da tabbacin cewa “ana ci gaba da mayar da martini kuma an karfafa tsarin tsaro.

” Ya kuma yi tir da gazawar kasashen duniya da kasancewar dubban sojojin Rwanda a kasar tare da bayyana kungiyar ta M23.

Wannan dai shi ne karon farko da shugaban na Kwango ke magana tun bayan harin da ‘yan tawayen suka kai a gabashin kasar a garin Goma.

Yayin jawabin shugaban na Kwango ya kuma ce suna goyon bayan hanyar tattaunawa.”

Félix Tshisekedi ya kuma yaba wa sojojin da suka fadi a fagen daga.”

Kungiyar M23 da ke samun goyon bayan sojojin Rwanda kimanin 3,000 zuwa 4,000, a cewar MDD, ta shafe fiye da shekaru uku tana fafatawa da sojojin Kongo a yankin, amma sun kutsa a cikin Goma babban birnin gabashin kasar a daren ranar Lahadi  zuwa Litinin ga watan Janairun nan inda suka mamaye tsatsa dama.

Akalla mutane 100 ne suka mutu sannan wasu sama da 1,000 suka jikkata, a cewar rahotanni daga asibitoci da dama.

Halin da ake ciki na jin kai yana da matukar damuwa, in ji Majalisar Dinkin Duniya, inda ta sanar da cewa dole ne a dakatar da rarraba kayan agaji saboda yanayin tsaro.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments