Shugaban kasar Iran Mas’ud Fizishkiyan ya yi kira da a kafa kawancen duniya da dukkanin kasashen musulmi za su shiga ciki, domin taimakawa mutanen Gaza, da sake gina yanki, tare da cewa, kasashen musulmi kadai za su iya sake gina yankin na Gaza tare da dawo da rayuwa a cikinsa.
A ganawar da ya yi da mambobin majalisar jagoranci ta kungiyar Hamas, anan Tehran ya yi jinjina ga shahidan kawancen gwagwarmaya, ya kuma yi murna akan nasarar da ‘yan gwgawarmaya su ka samu akan ‘yan sahayoniya.
Shugaban kasar ta Iran ya kara da cewa; Nasarorin da mutanen na Gaza su ka samu, sun hana makiya ‘yan sahayoniya cimma manufofin da su ka shata, duk da cewa adadin shahidan da aka samu suna da yawa.
Haka nan kuma ya ce; Abinda ya faru, ya cancanci a yi jinjina a gare shi, tare kuma da taya dukkanin mayaka da dukkanin mutanen Gaza murnar samun nasara.
A nasu gefen, ‘yan majalisar jagorancin na kungiyar Hamas, sun gode wa jamhuriyar Musulunci ta Iran da dukkanin ‘yan gwgawarmaya, da kuma taya su murnar nasarar da aka samu.