Shugaban kasar Iran Mas’ud Fizishkiyan ya bayyana cewa; Dukkanin batutuwan da Musulunci da kuma al’kur’ani maigirma suke bijiro da su, sun ginu ne akan ginshikin gaskiya da kuma adalci.
Shugaban kasar ta Iran ya kara da cewa; Idan har wadannan ginshikan biyu su ka zama ana aiki da su a cikin al’umma, to za a sami shiriya.
Shugaba Mas’ud Fizishkiyan ya kuma ce; A wannan lokacin muna da bukatuwa da koyar da dalibai da ‘ya’yanmu domin su kai ga mataki na koli na ilimi da kuma kyawawan halaye, ta yadda za su zama karfin madogara da hikima da kyawawan halaye a cikin al’umma.
Shugaban na kasar Iran ya kuma ce: Abubuwan da musulunci da kuma al’kur’ani suke bijiro da su, sun ginu ne akan ginshikai biyu da su ne gaskiya da kuma adalci a cikin dukkanin fagage.