Hukumar da take kula kai da komowar ziragen ruwa a duniya ( MarineTraffic) ta fitar da rahoton da yake cewa; Tun daga lokacin da Amurka ta sanar da fara aiki da killace tasoshin jiragen ruwan Iran a ranar 13 ga Aprilu, har zuwa 30 gare shi, jiragen ruwa da su ka kai 81 sun karya killacewar ta Amurka.
Rahoton ya ci gaba da cewa da akwai jirage 53 da su ka fito da kuma shiga tasoshin jiragen ruwan Iran ta hanyar ratsawa ta mashigar ruwan Hurmuz.
Haka nan kuma rahoton ya ce wadannan jiragen ruwa duk suna dauke da tutar Iran,kuma 11 daga cikinsu suna cikin wadanda Amurka ta kakabawa takunkumi.
Bugu da kari, daga cikin jiragen ruwan da su ka karya takunkumin ruwa na Amurka da akwai wasu 28 da ba na Iran ba ne, amma suna a karkashin takunkumin Amurka.
Iran dai tana daukar abinda Amurka take yi na killace tasoshin jiragen ruwanta da cewa, baya bisa doka, kuma daidai yake da fashi da makami a doron ruwa.
A ranar juma’ar da ta gabata shugaban kasar ta Amurka ya ce, abinda kasarta take yi daidai yake da ayyukan barayin ruwa. Ya bayyana cewa; Mun tsare jirgin ruwan Iran da man fetur da take dauke da shi. Kasuwanci ne mai riba sosai. Mu daidai muke da barayin ruwa.. Aikinmu ya yi kam da ayyukan barayin ruwa.”