Tashar talabijin din almayadin ta watsa labarin dake cewa, daga safiyar yau Alhamis zuwa yanzu, adadin Falasdinawan da su ka yi shahada sun haura 40,mafi yawancinsu daga yankin Khan-Yunus.
Tun da safiyar yau Alhamis ne dai sojojin HKI su ka fara kai hare-hare a yankuna mabanbanta na Gaza da su ka hada da Khan-Yunus. ‘Yan sahayoniyar sun yi amfani da manyan bindigogi da kuma jiragen sama na yaki.
Adadin wadanda aka tabbatar da sun yi shahada ya zuwa yanzu sun haura 40.
Sai dai wasu rahotannin da suke fitowa daga Gaza din sun ce, adadin shahidan ya karu zuwa 82.
Jiragen HKI suna kai wa yankin na Gaza hare-hare daga kduancinsa zuwa arewacinsa cikin hauka.
A Khan-Yunus ‘yan Sahayoniyar sun kai hari akan wasu gidaje 8 da mutane suke ciki, da ya yi sanadiyyar shahadar mutane 30 daga cikinsu har da kananan yara. Rahotannin da suke fitowa daga yankin sun ce an kai wasu kananan yara zuwa asibitin “Nasir” domin yi musu magani daga raunukan da su ka samu.
Wasu garuruwan da jiragen yakin HKI su ka kai wa hare-hare sun hada da “Khaza’a, Abisan alkabhirah, sai yankin Sanadhi’ da kuma kusa da sha-tale-talen Sadhra.
Sojojin mamayar HKI sun kuma kai wasu hare-haren akan sansanin ‘yan hijirar Falasdinawa a yankin Mawasi da yankin Abu Haddaf da garin alqararah.
A arewacin Gaza, sojojin HKI sun kai wasu hare-haren a kan wani gida na iyalan Shihab a garin Jabaliyah, da ya yi sanadiyyar shahadar mutane 7 da kuma jikkata wasu.