A ci gaba da tafka laifukan yakin da HKI take yi a Gaza,Fiye da Falasdinawa 60 ne su ka yi shahada a jiya Laraba.
A wani harin da sojojin mamayar su ka kai a yankin Jabaliya, Falasdinawa 5 sun yi shahada, yayin da wani adadi mai yawa su ka jikkata.
Wani jirgin sama maras matuki ya kai wani harin a unguwar “Shuja’iyya” wnada ya yi sanadin shahadar mutum daya, sai kuma wasu shahidan 4 a unguwar “Shari’u 5”, da kuma wasu shahidan 4 a garin “Bani-Suhaila”.
Wasu rahotannin sun ce, ‘yan sahayoniyar sun kai wasu hare-haren a garin ‘Abasan al-kabira’ da ya yi sanadin shahadar mutum daya da kuma jikkatar wasu masu yawa.
A yankin Qizan kuwa, ‘yan sahayoniyar sun kai hari akan mutanen da suke kokarin isa wurin da za su sami kayan agaji, tare da kashe 5 daga cikinsu a yankin kudu maso yammancin garin Khan-Yunus.
Ita kuwa hukumar yankin na Gaza ta sanar da cewa; ‘yan sahayoniyar sun kashe fararen hula 10 wadanda yunwa ci karfinsu, sannan kuma ta jikkata wasu 62 a wurin da aka ware na raba kayan agaji.
Sanarwar ta hukumar Gaza ta kuma ce; Yankunan da aka ware domin raba kayan agaji a karkashin Amurka da Isra’ila’ ya zama tarkon da ake kashe mutane a wurin.
A gefe daya ma’aikatar kiwon lafiya ta Gaza ta sanar da cewa; Sojojin mamaya sun kai wa asibitin tafi da gidanka na “Red-Cross” hari dake “Mawasi, a gundunar Khan-Yunus. “Yan mamayar sun kai harin ne adaidai lokacin da ake yi wa wadanda su ka jikkata magani.