Ma’aikatar kiwon lafiya ta Gaza ta sanar da cewa; Daga safiyar yau Alhamis zuwa yanzu adadin falasdinawan da su ka yi shahada sun haura 50.
Kididdigar ma’aikatar kiwon lafiya ta Gaza ta bayyana cewa a cikin sa’oi 24 da su ka wuce an kai shahidai 107 zuwa asibitoci daga cikinsu da akwai wasu shahidai 3 da aka fito da su daga cikin baraguzai; haka nan kuma wasu mutanen da adadinsu ya kai 247 sun jikkata.
Ya zuwa yanzu adadin wadanda su ka yi shahada tun daga ranar 7 ga watan Oktoba 2023 zuwa yanzu, sun kai dubu 53,762. Sai kuma wadanda su ka jikkata sun kai 1222, 197.
Daga sake dawo da yaki akan alummar Gaza, a ranar 18 ga watan Maris, adadin wdanda su ka yi shahada sun kai 3,613, sai kuma wadanda su ka jikkata da su ka kai 10,156.
Ma’aikatar kiwon lafiya ta Gaza ta kuma ce, da akwai wani adadi mai yawa na shahidai da suke a karkashin baraguzai da rashin kayan aiki ya hana masu aikin ceto isa gare su.
Adadin kananan yaran da su ka yi shahada tun daga fara yakin, fiye da shekara daya da rabi, sun kai 16,503.