Shugaban hukumar Spain Pedro Sanchez ya bayyana ” Isra’ila” da cewa; “Mai Kisan Kiyashi Ce,” wacce kasarsa ba za yi mu’amala da ita ba.
Fira ministan na kasar Spain ya bayyana hakan ne a matsayin mayar da martnni ga wani dan majalisar kasar daga yankin Catalonia, Gabrel Rovian yana wanda ya tuhume shi da cewa, yana huldar kasuwanci da Isra’ila,alhali tana yi wa mutanen Gaza kisan kiyashi.
Kafafen watsa labarun Spain sun ce wannan shi ne karon farko da firma ministan kasar ya bayyana abinda Isra’ila take yi da cewa kisan kiyasn kare dangi ne.
HKI ta fusata akan furucin da Fira ministan Spain tare da kiran jakadan kasar domin nuna masa rashin amincewa.