A yau Talata an sami karuwa da hauhawar farashin man fetur a kasuwannin duniya bayan karuwar hare-hare a tsakanin Yemen da Saudiyya.
Da misalin karfe; 6;30 a agogin GMT na yau Talata farashin danyen main a “Brent’ ya karu da Dala 1.25 da hakan ya kai shi Dala 98.25. Wannan shi ne farashi na koli da man fetur din ya kai tun a cikin watan Yuki na wannan shekara. A wancan lokacin an sayar da kowace gangar danyen man akan Dala 98.79.
Kamfanin dillancin labarun “Blumberg” ya nakalto wasu jami’ai suna cewa; harin daukar fansa da Ansarullah na kasar Yemen su ka kai a kudancin Saudiyya ya yi sanadiyyar dakatar da ayyukan hako mai da tace shi.
Wani mai Nazari akan harkokin hada-hadar man fetur na cibiyar “INZ” ya ce; Ba a tsammanin cewa yadda ake hako mai zai koma daidai daga nan har zuwa tsakiyar 2027.