Faransa Ta Zargi Isra’ila Da Karya Yarjejeniyar Tsagaita Wuta A Lebanon

Faransa ta zargi sojojin Isra’ila da karya yarjejeniyar tsagaita bude wuta da suka cimma da kungiyar Hizbullah har sau 52, ciki har da harin da

Faransa ta zargi sojojin Isra’ila da karya yarjejeniyar tsagaita bude wuta da suka cimma da kungiyar Hizbullah har sau 52, ciki har da harin da aka kai a ranar Asabar da ya yi sanadin mutuwar fararen hula 3 na Lebanon.

Rundunar sojin Isra’ila ta ba da hujjar kai hare-haren, tana mai cewa suna mayar da martani ne ga kungiyar Hizbullah.

To saidai shafin Ynet News, ya nakalto  Faransa, na cewa Isra’ila ta dauki matakin ne ba tare da tuntubar kwamitin kasa da kasa da aka dorawa alhakin sa ido kan yadda yarjejeniyar ta kasance ba.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ‘yan kasar Lebanon sun kuduri aniyar tabbatar da tsagaita bude wuta.

Jami’an Isra’ila sun kare matakin nasu, duk da haka suna mai cewa kwamitin sa ido na kasa da kasa ba zai fara aiki gaba daya ba kafin ranar Litinin ko Talata, kuma sun ce za su ci gaba da kai hare-hare har zuwa lokacin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments