Faransa Ta Mika Sansanin Soja Na “Abeche” Ga Gwamnatin kasar Chadi

Gwamnatin kasar ta Faransa ta janye sojojinta daga wannan sansani na garin “Abeche” tare da mika shi ga mahukuntan Chadi, da hakan ya sami halartar

Gwamnatin kasar ta Faransa ta janye sojojinta daga wannan sansani na garin “Abeche” tare da mika shi ga mahukuntan Chadi, da hakan ya sami halartar ministan tsaron kasar Chadi, da kuma jami’an sojan kasar Faransa.

Kwamandan sojan Faransa a yankin Sahel Kanar Boris Pomirol ya bayyana cewa; “Da akwai alaka mai karfi a tsakanin sojojin Faransan da mutanen wannan garin da hakan yake a matsayin shaida akan kawance mai dorewa a tsakanin bangarorin biyu.”

 Ya kuma kara da cewa; bayan gushewar shekaru masu yawa, a yau a Cahdi an sami sauyi, domin kasar Chadi ta bunkasa karfin da take da shi na iya fuskantar kalubalen tsaro dake gabanta. Mika wannan sansanin ga Chadi yana nuni da hakan.”

Haka nan kuma ya ce: “Janye sojojinmu ba ya nufin ban kwana tsakanin Chadi da  Faransa, yana nufin cewa sai mu kara haduwa.”

Shi kuwa ministan tsaron Chadi Issaka Maroua Djamous wanda ya yi maraba da matakin mika sansanin ga kasarsa, ya kara da cewa, wa’adin karshe na janyewar sojojin Faransa daga kasar shi ne 31 ga watan nan na Janairu, 2025.”

Garin Abeche dai yana a arewacin kasar Chadi ne, an kuma san shi a tsawon shekaru a matsayin matsugunin sojojin Faransa. Kuma a lokuta mabanbanta an sha yin Zanga-zangar ganin an kawo karshen zaman sojojin Faransa a cikin wannan sansanin, sai dai jami’an tsaron kasar ta Chadi sun sha murkushe masu yin zanga-zanga.

Wasu daga cikin manyan makaman sojojin na Faransa za a shiga da su ta kasa ne zuwa Kamaru, daga can kuma a dauke su ta ruwa zuwa Faransa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments