Tsohon shugaban kasar Faransa, Nicolas Sarkozy, ya fara zaman gidan yari na shekara biyar a gidan yarin La Santé da ke tsakiyar birnin Paris.
An same shi da aikata laifin hada baki wajen samun kudaden yakin neman zabensa na shekarar 2007 daga tsohon shugaban Libiya, Muammar Gaddafi.
Sarkozy ya musanta aikata laifin, kuma ya nemi a sake shi daga gidan yari yayin da yake neman daukaka kara.
Wannan dai shi ne karo na farko a tarihin jamhuriya ta biyar da wani tsohon shugaban kasar zai kwana a gidan yari.
Magoya bayansa sun taru da sanyin safiyar yau a wajen gidansa na Paris.
A shafin sa na sada zumunta ya yi wa magoya bayansa alkawarin cewa .gaskiya za ta yi nasara.
Za a tsare Sarkozy, wanda yake da shekaru 70 a sashen kebantattun fursunoni.
A tarihin Faransa, shugabanni biyu ne kawai suka taba zuwa gidan yari kafin shi da suka hada da Philippe Pétain, wanda ya yi hadin baki da Jamusawa a lokacin Yakin Duniya na Biyu, da kuma Sarki Louis na 16, kafin a kashe shi.