Minitsan harkokin cikin gidan kasar Faransa ya bayyana cewa adadin wadanda su ka shiga Zanga-zangar tsadar rayuwa a kasar a jiya Asabar sun kai 550,000.
Ministan harkokin cikin gidan na Faransa Laurent Nuñez-Belda wanda ya yi wannan sanarwar ya kuma kara da cewa: cewa a cikin birnin Paris kadai yawan masu Zanga-zangar sun kai 110,000, kuma an kame mutane 400.
A yayin gangamin da masu adawa da tsadar rayuwar su ka yi a birnin Paris na yi taho-mu-gama da ‘yan sanda.
Daga cikin abinda masu Zanga-zangar suke fada da shi da akwai karuwar farashin makamashi.
Jaridar “Guardian” ta Birtaniya da ta dauki rahoton abinda ya faru, ta ce matasa da dama sun sami raunuka da su ka yi kama da na yaki, saboda yadda ‘yan sanda su ka yi amfani da abubuwa masu fashewa wajen kokarin tarwatsa masu Zanga-zangar.
Masu kare hakkokin bil’adama kuwa suna yin gargadi ne akan karuwar yawan wadanda ake kamawa ba bisa dalili na doka ba, tare da zargin ‘yan sandan kasar da amfani da karfi mai yawa domin firgita da tsorata matasa.
Ita dai wannan Zanga-zangar ta Faransa ta faro ne daga dalibai da suke son ganin an kyautata yanayin karatunsu da wadata su da isassun malamai.