Search
Close this search box.

Falastinawa 39,677 Ne Suka Yi Shahada A Hare-Haren Isra’ila A Gaza

A ci gaba da kisan kare dangi da Sojojin Isra’ila ke ci gaba da yi a kan Falasdinawa a yankin zirin Gaza, tun daga ranar

A ci gaba da kisan kare dangi da Sojojin Isra’ila ke ci gaba da yi a kan Falasdinawa a yankin zirin Gaza, tun daga ranar 7 ga Oktoba ya zuwa yanzu Falastinawa 39,677 ne suka yi shahada, kamar yadda bayanan Ma’aikatar Lafiya a yankin suka tabbatar, sannan akasarin wadanda suka rasa rayukansu sakamakon hare-haren na Isra’ila a Gaza mata da kanan yara.

Wata sanarwa da ma’aikatar ta fitar ta ƙara da cewa zuwa yanzu kuma mutum 91,645 ne suka jikkata.

“Dakarun Isra’ila sun kashe mutum 24 tare da jikkata wasu 110 a “kisan kiyashi biyu’ da aka yi wa iyalai da dama a cikin awa 24,” in ji ma’aikatar. Ta ƙara da cewa “har yanzu akwai mutane da dama da ke binne a ƙarƙashin ɓaraguzai saboda masu aikin ceto sun gaza ciro su.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments