Falasdinu : ‘Yan jarida 222 aka kashe tun fara yakin Gaza

Bayanai daga falasdinu na cewa an kashe ‘yan jarida 5 na Falasdinawa a wasu hare-hare daban-daban da Isra’ila ta kai a zirin Gaza, lamarin da

Bayanai daga falasdinu na cewa an kashe ‘yan jarida 5 na Falasdinawa a wasu hare-hare daban-daban da Isra’ila ta kai a zirin Gaza, lamarin da ya kai adadin ma’aikatan yada labaran da aka kashe tun farkon yakin Isra’ila a zirin Gaza zuwa 222.

Daga cikin wadanda harin ya rutsa da su har da dan jarida mai daukar hoto Aziz al-Hajjar, da matarsa, da ‘ya’yansu, wadanda aka kashe a ranar Lahadi, lokacin da jiragen yakin Isra’ila suka kai hari a gidansu da ke unguwar Saftawi a arewacin Gaza.

A gefe guda kuma, an kashe dan jarida Ahmad al-Zinati tare da matarsa, Nour al-Madhoun, da ‘ya’yansu, Mohammad da Khaled, a lokacin da aka kai wa tantin su hari a Khan Younis a yammacin ranar Asabar.

Shahadar wadannan ‘yan jarida na zuwa ne kwanaki biyu kacal bayan mutuwar Ahmed al-Halou, wani dan jarida da ke aiki da kafar yada labaran birnin Quds, wanda aka kashe a wani harin da Isra’ila ta kai a zirin Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments