Falasdinu: Mahmud Abbas Ya Nada Magaji Da Kuma Mataimakasa

Shugaban Palasdinu da kuma kungiyar kwatar yencin falasdinawa PLO Mahmud Abbas ya nada magajinsa da kuma wasu mataimaka. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran,

Shugaban Palasdinu da kuma kungiyar kwatar yencin falasdinawa PLO Mahmud Abbas ya nada magajinsa da kuma wasu mataimaka.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran, ta bayyana cewa Abbas dan shekara 89 ya nada mataimakinsa ne bayan taron majalisar gudanarwa ta gwamnatinsa  a makon da ya gabata.

Labarin ya kara da cewa kasashen yamma da yankin sun dade suna takurawa Abbas kan ya nada mataimaki da kuma wasu mataimaka sabuda rawar da gwamnatinsa zata taka bayan yakin gaza.

A yau ne majalisar zartarwa ta amince da nada Hussein Al Sheikh a matsayin mataimakin shugaban majalisar da kuma mataimakin shugaban kasa a lokaci guda.

Kamfanin dillancin labarai na gwamnatin Falasdinawan WAFA, ya bayyana cewa gwamnatin Abbas ce da hakkin sa hannu a kan yarjeniyoyi da suka shafi Falasdinu, a madadin dukkan kungiyoyin Falasdinawa, banda wadanda su ka dauke da makamai suna yakar HKI, wato Hamas da kuma Jihadul Islami a Gaza.

Mr Al Sheikh, dan shekara 64 a duniya na hannun daman Abbas ne a kungiyarsa ta fatah.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments