Rundunar “Sarayal-Kudus” ta kungiyar jihadul-Islami ta harba makamai masu linzami akan sansanonin ‘yan share wuri zauna na “Asqalan” da “Ushdud”.
A jiya Talata ne dai rundunar ta Sarayal-Qudus’ ta sanar da harba makamai masu linzamin kaan sansanonin ‘yan share wuri zauna, a matsayin ci gaba da mayar da martani ga hare-haren wuce gona da irin na HKI akan al’ummar Falasdinu.
Sanarwar da rundunar ta fitar ta kunshi cewa: Harin nata yana a matsayin mayar da martani ne akan kisan kiyashin da HKI take yi wa al’ummar Falasdinu a Gaza.
A wani labarin na daban, rundunar “Kassam” ta kungiyar Hamas ta sanar da cewa ta yi taho-mu-gama da sojojin mamaya a unguwar “Shuja’iyya” dake gabashin birnin Gaza.
Sojojin HKI suna ci gaba da yi wa al’ummar Gaza kisan kiyashi, haka nan kuma killace yankin da hana shigar da kayan agaji da su ka hada abinci da magani.