Sojojin HKI suna ci gaba da kai hare-hare a sassa daban-daban na yankin zirin Gaza da su ka hada da sansanonin ‘yan hijira da kuma rusa gidajen da su ka saura a tsaye.
Tashar talabijin din ‘almayadin” ta bayyana cewa; An sami shahidai 7 da safiyar yau Laraba, bayan harin da ‘yan sahayoniyar su ka kai akan wani gida da yake a Deir-Balah,dake tsakiyar zirin Gaza.
A can sansanin ‘yan hijira dake kusa da filin wasa na ‘al-Anan’ kuwa mutane 4 ne su ka jikkata.
A yankin Safdawi dake cikin birnin Gaza, jiragen yakin HKI sun kai hare-hare akan wani gida wanda ya haddasa gobara, da kuma shahadar mutane 8.
A unguwar “Shuja’iyya” sojojin na mamaya sun rushe gidaje da dama.
Gabanin wannan lokacin, an sami wasu shahidan 3 da kuma jikkatar mutane 46 a kusa da cibiyar da Amurka da Isra’ila su ka ware domin raba kayan abinci.
Kididdiga ta karshe wacce ma’aikatar kiwon lafiya ta Gaza ta fitar ta bayyana cewa; adadin Falasdinawan da su ka yi shahada daga 7 ga Oktoba, sun kai dubu 45,56, sai kuma wadanda su ka jikkata da sun kai 129, da kuma 123.