A daidai lokacin da sake bude yaki a Gaza ya cika kwanaki 57,sojojin HKI suna ci gaba da kai hare-hare akan al’ummar Gaza da hakan ya yi sanadiyyar shahadar Falasdinawa da dama.
Cibiyar watsa labaru ta Falasdinu ta sanar da cewa; Sojojin na HKI sun kai hare-hare masu yawa a sassa mabanbanta na gaza wanda ya fara tun daga watan Maris, da hakan ya kara jefa Falasdinawa cikin wahala, bayan yunwar da suke fama da ita.
Da safiyar yau Talata sojojin na HKI sun kai hare-hare sau 3 a garin Abasan a gabashin Khan-Yunus.
A cikin birnin Gaza kuwa sojojin na HKI sun baje wasu gidaje da kasa a karo na uku.
A garin Khan-Yunsu wani matashi mai suna Amid Hamdun al-Qudrah, ya yi shahada.
A unguwar “Shuja’iyyah” ma wani Bafalasdine mai suna Muhammad Mu’in al-Ja’abari ya yi shahada sanadiyyar raunin da ya samu a harin baya.
A unguwar “Zaytun” kuwa sojojin na HKI su kai hare-hare ne har sau 8 a yau Talata.
A daren jiya wasu Falasdinawa 3 daga iyali 1 sun yi shahada a cikin tantin ‘yan hijira a yankin ‘al’amudi’ a arewacin Gaza.