Falasdinawa Da Dama Sun Yi Shahada A Wurare Mabanbanta Na Gaza

A daidai lokacin da yakin Gaza yake cika kwanaki 436, sojojin mamaya sun ci gaba da yi wa Falasdinawa  kisan kiyashi a wurare daban-daban na

A daidai lokacin da yakin Gaza yake cika kwanaki 436, sojojin mamaya sun ci gaba da yi wa Falasdinawa  kisan kiyashi a wurare daban-daban na zirin Gaza. Daga cikin yankunan da su ka kai wa hari da akwai sansanin ‘yan hijira na Khayyam da hakan ya yi sanadiyyar samun shahidai.

Daga safiyar yau Lahadi zuwa  marece, an sami shahidai 25 mafi yawancinsu a arewacin Gaza.

Tashar talbijin din ‘almayadin’ ta ambaci cewa an gano gawawwakin shahidai 11 a cikin birnin Gaza a tsakanin daren jiya Asabar, zuwa safiyar yau Lahadi.

 Bugu da kari injinan yakin HKI sun kai wasu hare-hare akan “Beit-Hanun” dake arewacinn Gaza, tare da tilasta wa ‘yan hijira a cikin makarantar “Khalil Uwaidha” ficewa daga cikinta, da hakan ya yi sanadin shahadar mutane 15 da kuma jikkata wasu da dama.

Har ila yau, ‘yan mamayar sun kai wasu hare-haren akan yankin Sheikh zayid dake Beit-Lahiya, kamar kuma yadda su ka ruguje wasu gidaje a yankunan ‘Sudaniyyah’ da Karamah, duk a arewacin Gaza.

Sojojin mamayar sun yi amfani da jirgin sama maras matuki wajen kai hari akan gidajen mutane dake daura da asibitin “Kamal Adwadan’ shi ma a arewacin Gaza.Mutane biyu ne su ka yi shahada, yayin da wasu su ka jikkata sanadiyyar wannan harin.

Wasu Falasdinawan 3 sun yi shahada a harin da sojojin na Isra’ila su ka kai a unguwar “Zaytun” dake kudancin Gaza. A tsakiyar Gaza kuwa, ‘yan mamayar sun kai wani harin akan yankin Abu Iskandar da shi ma ya yi sanadiyyar shahadar mutane da dama da jikkata wani adadi mai yawa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments