A wani sabon hari da sojojin HKI su ka kai wa asibitin Kamal Adwan dake arewacin Gaza, sun kashe Falasdinawa da dama yayin da wani adadi mai yawa ya jikkata.
Rahotannin da suke fitowa daga Falasdinu sun ambaci cewa a kalla Falasdinawa 30 ne su ka yi shahada a yau Juma’a sanadiyyar harin da sojojin Sahayoniya su ka kai wa Asibitin, yayin da wasu masu yawa su ka jikkata.
Shugaban asibitin na “Kalam Adwan” Hisam Abu Safiyyah, ya ce, sojojin mamayar sun kuma kutsa cikin asibitin inda su ka kama ma’aikatan asibitin da dama, haka nan kuma ‘yan hijira da aka rusawa gidajen su ka sami mafaka a cikin wasu sashe na asibiti.
Wannan dai ba shi ne karon farko da sojojin HKI suke kai wa asibitocin Gaza hari ba, inda a shekarar da ta gabata su ka kashe mutane 500 a tashi daya a asbitin “Ma’amadani”
Mafi yawancin asibitocin yankin Gaza sun daina aiki saboda hare-haren sojojin HKI da kuma kame ma’aikatansa da suke yi.