Falasdinawa Biyu Sun Yi Shahada A Nablus Da Khalil

Da safiyar yau Litinin  Falasdinawa biyu sun yi shahada a Nablus da garin al-Khalil, na farko dan shekaru 17, na biyun kuwa dan shekaru 35.

Da safiyar yau Litinin  Falasdinawa biyu sun yi shahada a Nablus da garin al-Khalil, na farko dan shekaru 17, na biyun kuwa dan shekaru 35.

Ma’aikatar kiwon lafiya ta Falasdinawa  ta ce, matsashin dan shekaru 17 ya cika ne saboda raunukan da ya samu a yayin taho mu gama da sojojin sahayoniya da su ka yi kutse a garin Beit Forik a gabashin garin Nablus.

Shi kuwa dan shekaru 35 din ya yi shahada ne sanadiyyar bude masa wuta da wani dan share wuri zauna ya yi masa a mashigar garin al-khalil.

Kungiyar Agaji ta “Hilal-Ahmar” ta ce;An hana ma’aikatansu isa wurin da aka aka jikkata Bafalasinen gabanin shahadarsa, kuma ‘yan share wuri zauna sun killace yankin.

A gefe daya sojojin HKI sun yi kutse acikin garuruwan Sa’ir, da shuyukh da suke a arewacin Khalil a jiya da dare.

Sojojin HKI suna ci gaba da kai wa Falasdinawa hare-hare a yammacin kogin Jordan, tare kuma da kwace musu gonaki sa gidaje domin gina matsugunnan ‘yan share wuri zauna.

Ofishin Yada Labarai na Gwamnatin Gaza Ismail al-Thawabteh ya ce tun bayan cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza wadda ta fara aiki a ranar 10 ga Oktoba,yan mamayar sun keta ta har sau 194.

Jami’in na Hamas ya ce sojojin Isra’ila sun sha  wuce gona da iri suna kai hare-hare ta sama da rusa gidaje, wanda ya haifar da mutuwar fararen hula da raunuka.

A cewar ofishin yada labarai, daga ranar 10 ga Oktoba zuwa karshen watan, manyan motoci 3,203 ne kawai suka shiga Gaza daga cikin motoci 13,200 da ake sa ran za su shiga karkashin yarjejeniyar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments