Falasdinawa 86 Ne Su Ka Yi Shahada A Cikin Sa’o’i 24 Da Su Ka Gabata

Ma’aikatar kiwon lafiya ta Falasdinu ta sanar da cewa adadin wadanda su ka yi shahada a cikin sa’o’I 24 da su ka wuce, sun kai

Ma’aikatar kiwon lafiya ta Falasdinu ta sanar da cewa adadin wadanda su ka yi shahada a cikin sa’o’I 24 da su ka wuce, sun kai 86, yayin da wadanda su ka jikkata kuwa sun kai 287.

Asibitocin yankin na Gaza sun karbi wannan adadin na  shahidai da kuma wadanda su ka jikkata, suna karbar magani.

Ma’aikatar harkokin kiwon lafiyar ta Falasdinawa ta kara da cewa ya zuwa yanzu jumillar Falasdinawan da HKI ta kashe tun daga 7 ga watan Oktoba na 2023 zuwa yanzu sun haura dubu 50.

Bugu da kari a halin da ake ciki da akwai gawawwakin shahidai masu yawa da suke kwance a karkashin baraguzan gidajen da HKI ta rushe da mutane a cikinsu, da kuma wadanda ta kashe akan hanya a lokacin da suke tafiyar zuwa inda za su sami mafaka.

Yankunan da HKI ta tsananta kai wa hare-hare a yau sun hada Khan-Yunus da kuma Arewacin Rafah.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments