Bayanai daga Falasdinu na nuni da cewa akalla Falasdinawa 47 ne sukayi shahada a ranar Asabar din nan a hare-haren da Isra’ila ta kai ta sama da jiragen yaki a Gaza yayin da sojojin suka sabunta bukata ga mazauna birnin da su fice daga birnin su koma kudu.
A wani labarin kuma harin da Isra’ila ta kai ta sama ya kashe Falasdinawa takwas a Gaza, ciki har da yara biyu ,a cewar hukumomin lafiya.
Wata majiyar lafiya ta shaida wa kamfanin dilancin labaren Anadolu cewa, yara biyu ne suka mutu a lokacin da jiragen yakin Isra’ila suka yi ruwan bama-bamai a makarantar Al-Mu’tasim a kusa da filin wasa na Yarmouk da ke birnin Gaza.
Haka zalika wani bafalasdine ya mutu a wani harin da Isra’ila ta kai kan wani taron fararen hula da ke kusa da Asibitin Jordan a unguwar Sabra da ke Gaza.
A halin da ake ciki adadin falasdinwan da sukayi shahada tun daga watan Oktoban 2023, ya haura samda 65,200 a yakin da Isra’ila ke yi a Gaza, yawancinsu mata da yara.