Falasdinawa 30 sun yi shahada a Wani harin Isra’ila kan wata makaranta

Bayanai daga Falasdinu na cewa wani hari da jiragen yakin Isra’ila suka kai cikin dare a wata makarantar Gaza dake zaman matsugunni ga masu neman

Bayanai daga Falasdinu na cewa wani hari da jiragen yakin Isra’ila suka kai cikin dare a wata makarantar Gaza dake zaman matsugunni ga masu neman mafaka ya yi sanadin shahadar Falasdinawa 30, ciki har da yara da dama, a cewar jami’an kiwon lafiya da na fararen hula.

Da sanyin safiyar yau litinin ne sojojin gwamnatin Isra’ila suka kai hari a makarantar Fahmi al-Jarjawi da ke yankin Daraj na zirin Gaza, inda daruruwan iyalai da suka rasa matsugunansu daga garin Beit Lahia da ke arewacin kasar da Isra’ila ke fama da hare-haren bama-bamai suka samu mafaka.  

Hukumar tsaron farar hula ta Gaza ta ce masu aikin ceto sun tsamo gawarwakinmutum 20 daga makarantar, ciki har da yara da dama.

A cewar majiyoyin yankin, wadanda harin ya rutsa da su sun hada da Mohammad al-Kasih, shugaban bincike na ‘yan sandan Hamas a arewacin Gaza, da kuma matarsa ​​da ‘ya’yansa.

Ma’aikatar lafiya ta Falasdinu ta kuma bayar da rahoton cewa, wani hari ta sama da Isra’ila ta kai kan wani gini da ke titin Thawra a birnin Gaza jim kadan kafin harin makarantar.

A cewar ma’aikatar lafiya ta Falasdinu, kusan Palasdinawa 54,000 ne aka kashe tun fara fara farmakin Isra’ila a ranar 7 ga watan Oktoba, yawancinsu mata da yara.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted