Falasdinawa 1500 Ne Su Ka Zama Makafi Sanadiyyar Yaki

Shugaban Asibitin ido dake Gaza, Dr. Abdussalam Sabah, ya sanar da cewa, adadin Falasdinawan da su ka rasa ganinsu sanadiyyar yaki sun kai 1500. Dr.

Shugaban Asibitin ido dake Gaza, Dr. Abdussalam Sabah, ya sanar da cewa, adadin Falasdinawan da su ka rasa ganinsu sanadiyyar yaki sun kai 1500.

Dr. Abdussalam ya kuma yi gargadin cewa da akwai wasu Falasdinawa da sun kai 4000 da suke fuskantar barazanar rasa idanunsu saboda rashin kayan aiki a asibiti da kuma magani.

Likitan na asibitin idanun Gaza, ya kara da cewa; Rashin kayan aiki a asibitin domin yin tiyatar ido, yana yin barazanar tsayuwar aikin asibitin baki daya.

Dr. Abdussalam ya kara da cewa; A halin yanzu almakashi 3 kadai ake da shi a asibitin, irin wanda ake amfani da shi domin yin tiyatar ido.

Da dama daga cikin masu lalurar idanun sun same ta ne sanadiyyar fashewar abubuwa masu karfi na hare-haren HKI dake da bukayuwa da kayan aiki na musamman.

Haka nan kuma ya ce, matukar kungiyoyin kasa da kasa ba su tsoma baki ba, to nan gaba kadan Asibitin zai sanar da durkushewarsa.

A wani labarin mai alaka da wannan, ma’aikatar kiwon lafiya ta Gaza ta sanar da cewa, da akwai karancin magunguna a yankin,kuma wadanda ma su ka saura suna ci gaba da yin kasa sosai.

Har ila yau ta ce, da akwai nau’oin da sun kai kaso 65% na magunguna da babu ko da kwaya daya da ya saura. Haka nan muhimman magununan da ake da bukatuwa da su a cikin yankin sun kare kakaf da kaso43%.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments